Bani Da Hannun Cikin Matsalar Saraki - Buhari

Shugaban Muhammadu Buhari ya musanta kanshi da binciken da CCB da kotun CCT sukayi ma Bukola Saraki.
Shugaba Muhammadu Buhari da Bukola Saraki
Garba Shehu Mai taimaka ma shugaban kasa ya a ranar Lahadi 20 ga watan Satumba ya bayyana cewa shugaban kasa baya da hannun cikin binciken Saraki. Sannan kuma ya bayyana cewa doka bata yadda wata Kotu ta ba Kotun CCT umurni ba.
“A matsayin ta da Kotu mai cikakken iko kamar kowace, Doko ce ta kafa ta domin kula da bayyana kaddarori na karya, yaudara da kuma algushu. Wannan abu ne na shari’a dan haka Fadar Shugaban Kasa bata da hanniu a ciki.
“Idan Wani bai ji dadin abun ba, toh sai ya nuna ta hanyar bin shari’a. Sai ya dauki lauyoyi masu kyau domin suje su bada shaidar gaskiyar shi.
“Shugaban kasa ya sha alwashin bin tsarin doka. Ya fadi bala adadin cewa yaki da rashawa ba zaya kyale wani mutum ba.”
Shehu ya bayyana cewa shugaban kasa babu ruwan shi a ciki. Kuma babu yadda za’ayi ya hana shari’a yin aikin ta.
“Wannan irin abubuwannan nan ne wadanda CCB da CCT ke kula dasu lokaci – lokaci. Akwai dayawa irin su. Shugaban kasa ya dauki rantsuwa, kuma ba zaya saba ma wannan rantsuwar ba.”
Sanatoci 50 ne suka hadu a Abuja domin tattaunawa akan abun. Mataimakin shugaban masu rinjage, Bala Ibn Na’Allah ya jagoranci zaman.
Saraki kuma ya karyata cewa zaya canza sheka daga APC zuwa PDP.
Naij.com has launched its Hausa service. Please help us to improve our quality by rating the clarity of language in the article above
Thanks For You Reading The Post We are very happy for you to come to our site. Our Website Domain name http://gurusfanz.blogspot.com/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment