Ministocin Jonathan Sun Ki Maido Da Motocin Su
Wasu daga cikin ministocin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan har yanzu basu maido da motocin da suke amfani dasu ba a lokacin da suke ministoci.
Motocin sun hada da motar rakayi ta Pilot wanda suke wucewa kan hanya ba tare da an tsaida su ba.
Gwamnatin tarayya tayi kira a gare su da su maido da motocin. Wasu daga cikin su sunyi ikirarin cewa basu maido da motocin ba saboda sakwai kudaden albashin su da gwamnati bata biya ba.
Tsofaffin Ministoci 15 har yanzu basu maido da motocin ba. Gwamnatin tarayya ta umurci sakatarorin ma’aikatu da su rubuta ma tsofaffin ministocin da su maido da motocin. Gwamnati ta gargade su da su maido ko ku fuskanci hushin ta.
Wata majiya daga fadar shugaban tace:
”Har yanzu akwai Ministoci 15 wadanda basu maido da motocin su ba musamman SUV da kuma motoci na Pilot wadanda suke wuce wa kan hanya.
“Wasu basu gam ba saboda suna bin gwamnati kudaden alawuns har na tsawon wata 8 wadanda ba a biya ba. Bamu da zabi sai da mu rubuta masu dasu maido da motocinko kuma mu sake sayen wasu ga sabbin ministocin da za’a nada.
“Wasu na ganin cewa sun cancanci haka saboda ba’a biya su mudaden su ba. Wani tsohon Minista ya bayyana cewa. Wane Motoci kuma bayan ba a biya wadansun mu ba har na tsawon wata 8. Ahi kan shi tsohon shugaban kasa Jonathan, da kuma mataimakin shi Namadi Sambo ba’a biya su ba. Mun bar biyan ne ga gwamnatin Buhari wanda ta shigo domin ta biya.
“Wasu daga cikin mu sun bar kasar, wasu kuma na canza wajaje dabam dabam. Amma wasu har sun fara maido da motocin.”
Thanks For You Reading The Post
We are very happy for you to come to our site. Our Website Domain name
https://gurusfanz.blogspot.com/.
Newer Posts
Newer Posts
Older Posts
Older Posts
Comments